Chukwueze ya haskaka a wasan da Villarreal ta doke Madrid

0
142

Dan wasan Nijeriya, Samuel Chukwueze da ke taka leda a Villarreal ya taimaka wa kungiyar wajen doke Real Madrid da ci 3-2 a gasar La Liga.

An buga wasan ne ranar Asabar a gidan Madrid wato Santiago Bernabeu.

Tun da farko dan wasan Villareal Pau Torres ya yi kuskuren zura kwallo a ragar kungiyarsa a minti 16 da fara wasa.

Amma a minti na 39 Chukwueze ya danna cikin gidan Real Madrid ya zura musu kwallo.

A minti na 48, Real Madrid ta sake zura ƙwallo a ragar Villarreal ta hannun Vinicius Junior.

Sai kuma a minti na 71 lokacin da Jose Luis Morales ya zura ƙwallo a ragar Madrid lamarin da ya mayar da wasan 2-2.

Karawar ta cigaba a haka har lokacin da Chukwueze ya harba ƙwallo a ragar Madrid a minti na 80, lamarin da ya bai wa Villarreal nasara a gidan Madrid.

Wannan sakamakon dai ya kara saka Madrid cikin rashin tabbas a kokarinta na sake riƙe kogin La Liga a bana.

Babbar abokiyar hamayyarta Barcelona tana ta É—aya a teburi da maki 71 yayin da Real Madrid ke bin ta da maki 56.

Ita kuwa Villarreal tana ta biyar a teburin da maki 47, ƙasa da Real Sociedad, inda inda wani ɗan Nijeriya Umar Sadid yake.

Ita dai Real Sociedad ita ce ta hudu a teburin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here