Messi ne ya zura kwallo a raga a minti na 26 da fara wasan wanda hakan ya baiwa ‘yan wasan na Paris nasara.
A yanzu dai dan wasan da ya lashe kofin duniya na kasar Argentina ya zura kwallaye 702 a manyan kungiyoyin Turai biyar, wanda ya zarce Ronaldo da daya.
Messi ya kai matsayin a wasanni 105 a kasa da tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid.
Dan wasan mai shekaru 35 ya zura kwallaye 672 a wasanni 778 a lokacin yana Barcelona.
Dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau bakwai a yanzu ya ci wa PSG kwallaye 30, inda ya buga wasanni 68 ciki har da wasan Nice.