Yaya makomar Messi bayan an fara yi masa ihu a PSG?

0
142
Sannan damar daukar Kofin Ligue 1 da PSG ke ita tana kara dusashewa, bayan Kungiyar Lyon ta yi mata daya mai ban haushi a gida a ranar Lahadin da ta gabata.

Kyaftin din na Ajantina bai taka rawar gani ba a wasan, inda karo biyu ke nan a jere da aka doke PSG a gida, kuma Messi bai ci kwallo ba.

PSG na fatar daukar Kofin Ligue 1 karo na 11 kuma na tara a kaka 12 bayan da attajiran Katar suka saye kungiyar.

Yanzu tazarar maki shida ke tsakaninta da masu biye da PSG, wato kungiyoyin Lens da Marseille ana saura wasa tara a kare gasar.

Wannan ce kaka mafi muni da PSG ta fuskanta tun shekarar 2001, kuma wasan gaba da kungiyar za ta yi, shi ne a gidan Nice, wadda ba a doke ta ba tun watan Janairun 2023.

Ke nan Kofin Ligue 1 kadai PSG ke fatar dauka a kakar nan, bayan an yi waje da ita a Zakarun Turai da French Cup.

Duk kakar da aka fitar da PSG daga Zakarun Turai sai su koma daukar sauran wasanni da rashin mahimmaci,” in ji Bincent Duluc kamar yadda BBC ta ruwaito daga L’Ekuipe.

Wasu na ganin cewa yi wa Messi ihu a lokacin da ya taba kwallo bai kamata ba, wanda shi ne ya ja ragamar Ajantina ta lashe Kofin Duniya a Katar a bara.

Wasu magoya bayan PSG kan dora alhakin rashin kokarin kungiyar a kan Kyaftin din na Ajantina, inda kuma suke ganin har yanzu ba a kammala gina PSG yadda ya kamata ba.

L’Equipe ta ce ihun da ake yi wa Messi ya shafi yawo da yake yawan yi shi kadai a fili, maimakon guje-guje da sa kwazon karbar kwallo daga abokan karawa.

To sai dai ba a wannan kakar Messi ya fara yawan yawo a cikin fili ba – wani bincike da aka gudanar a gasar Kofin Duniya a Katar, ya nuna Messi ya yi tafiyar kilomita 14 kawai a cikin fili a wasa uku na rukuni.

Sai dai wasu na ganin cewa yanzu shekarun Messi sun ja, inda a cikin watan Yuni mai zuwa zai cika shekara 36 a karshen yarjejeniyarsa da PSG, bayan kaka biyu.

Yanzu zabi ya rage wa PSG, ko za ta tsawaita zaman Messi, wanda shekaru suka ja masa tare da ci gaba da biyansa Dala miliyan 43.6 duk shekara a lokacin da UEFA ta sa mata ido kan kashe kudin kungiyar daidai da abin da ta samu.

Kocin PSG, Christophe Galtier ya ce, mutane suna daura nauyi da yawa a kan Messi da Mbappe, inda ya ce duk da ’yan wasan suna kokari da zarar an samu rashin nasara sai a rika dora alhakin haka a kansu.

Sai dai ana ganin ba laifin magoya bayan kungiyar ba ne, domin a kakar bana baki daya Messi ba ya nuna kwarewa da bajinta.

A wasa 36 da ya buga wa kungiyar, kwallo shida kawai ya zura, wanda hakan na zuwa ne a tsakanin lokacin da ya lashe Kofin Duniya.

A daya bangaren kuma, duk da cewa Ronaldo ya koma Saudiyya da taka leda, inda ake ganin karamar gasa ce, dan wasan na Portugal ya zura kwallo 11 a wasa 10.

Ana zargin akwai tsama tsakanin ’yan wasan PSG, inda kungiyar za a iya cewa yanzu tana hannun dan wasan Faransa Mbappe da rahotanni ke nuna ba ya son kasancewar Neymar Jnr a kungiyar, sannan bai cika girmama Messi ba, saboda ya fi ganin Cristiano Ronaldo a matsayin abin koyi a gare shi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Kungiyar Al Hilal ta Saudiyya ta taya Messi a kan Fam miliyan 400 duk shekara, inda zai kasance yana karbar albashi kusan ninkin na Cristiano Ronaldo a Kungiyar Al Nassr ta Saudiyya.

Sai dai kuma fitaccen dan jaridar wasanni, Fabrizio Romanio ya ruwaito cewa, Messi ya fi sha’awar ci gaba da zama a Turai, inda yanzu haka tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona ke ci gaba da zawarcinsa.

Idan Messi ya koma Saudiyya, zai sake hadewa da abokin karawarsa, Ronaldo domin su ci gaba da fafatawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here