Birtaniya za ta daina ɗaukan likitoci daga Najeriya

0
143

Birtaniya ta sanya sunan Najeriya a cikin jerin ƙasashen da ba za ta rinƙa ɗaukan likitoci da masu kula da masu rauni daga ƙasar ba.

Birtaniyar ta ɗauki matakin ne bayan sabunta ƙa’idojinta na ɗaukan ma’aikata daga ƙasashen ƙetare.

A yanzu sunan Najeriya ya faɗa cikin waɗanda aka sanya wa launin ja ko ɗorawa, wanda yake fitowa daga Hukumar Lafiya ta Duniya.

Jerin ƙasashen wanda WHO ke sabuntawa bayan shekaru uku na nufin cewa ba za a ɗauki jami’an lafiya daga irin waɗannan ƙasashe ba.

Hakan na nufin cewa Najeriya ba ta da isassun likitoci ko ma’aikatan lafiya da take buƙata, saboda haka bai kamata su riƙa samun raguwar ma’aikatan ba.

Sabunta jerin sunayen da Birtaniyar ta yi tamkar biyayya ce ga shawarar Hukumar Lafiya ta Duniya.

A yanzu Najeriyar ta shiga jerin ƙasashe 55 waɗanda ba za a iya ɗaukan jami’an lafiya daga cikinsu ba.

Sai dai kundin ƙa’aidojin aikin da Birtaniyar ta fitar ya ce ƙasashen da ke cikin jerin waɗanda lamarin ya shafa za su iya fita daga jerin bayan tattaunawar fahimtar juna tsakanin ƙasa da ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here