Sojoji sun sha artabu da ‘yan bindiga a Katsina

0
106

Sojoji sun yi artabu da Ƴan Bindiga a Garin Ɗanmarke.

Jami’an rundunar sojojin Najeriya sun ce sun yi ɗauki-ba-daɗi da wasu hatsabiban ƴan bindiga a ƙauyen Ɗanmarke dake cikin ƙaramar hukumar Ƙanƙara ta jihar Katsina.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwar manema labarai da jami’in yaɗa labaran rundunar na bataliyar ‘Hadarin Daji’, Manjo Janar Musa Ɗanmadami ya fitar.

A cewar sanarwar, an yi artabun ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata 8 ga watan Afrilu,

Sanarwar ta cigaba da cewa, a yayin artabun, sojojin sun samu nasarar kashe ɗan ta’adda ɗaya sannan suka fatattaki ƴan bindigar tare da ƙwace bindigogi 2 kirar AK-47 da shanu 150 da kuma tumaki 40 da dai sauran su.

A wani labarin makamancin wannan, sojojin sun kashe wasu ƴan bindigar kuma a wani samame da suka kai cikin dajin jihar Zamfara a Ƙauyukan Chabi da Ƴartasha dukkan su a karamar hukumar Maru.

A can ma, jami’an sojojin sun kashe ƴan bindiga 2 tare da kama ɗaya daga cikin su a raye

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here