Isiya Danwasa: Gwamna El-Rufai ya yaba wa sojoji kan kashe kasurgumin dan bindiga a Kaduna

0
139

Gwamnan jihar Kaduna malam Nasir El-Rufai ya yaba wa sojojin rundunar Operation Forest Sanity kan nasarar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan fashin daji Isiya Danwasa.

Wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta jihar ta fitar ranar Talata ta ce Isiya Danwasa ya dade yana kashe-kashe da satar mutane da satar dabbobi a fadin jihar.

“Danwasa ya gamu da ajalinsa ne a yayin wani kwanton bauna da aka shirya a yankin Sabon Birni da ke karamar hukumar Igabi.

“Gwamna El-Rufai ya yaba wa sojojin kan wannan aiki nasu na bajinta da suka yi da har ya jawo mutuwar Danwasa da wasu na kusa da shi,” in ji sanarwar.

Gwamna Nasir ya kuma roki jama’a da su ci gaba da bai wa jama’ian tsaro bayanai don kara samun nasara.

Kazalika wata sanarwar ta daban da hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta fitar ranar Talatar ta ce a yayin wannan aiki sojoji sun kama wani dan aiken shugaban ‘yan bindiga a yankin Mando da ke karamar hukumar Igabin jihar Kadunan.

 

 

Sanarwar ta ce bayan wasu bayanan sirri da dakarun tsaron Nijeriya suka samu, jami’an da ke kai farmaki na rundunar “Tsaftace Dazuka” tare da hadin gwiwar Dakarun Musamman na Rundunar Tsaro sun kama yaron a yayin da aka aike shi sayo harsashi 1,000 masu girman 7.62mm.

Jami’an sojin sun kuma samu nasarar kwato bindiga biyu kirar Ak47 da jigidar harsasan AK47 shida da harsasai 250 masu girman 7.62mm da kayan tsibbu da kuma kudi naira 200,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here