LabaraiLabaran Duniya Kwastam sun kama manyan dauri 400 na tabar wiwi a Nijar By Adam Usman - April 11, 2023 0 99 FacebookTwitterPinterestWhatsApp Hukumar Kwastam a Jamhuriyar Nijar ta kama miyagun kwayoyi a yankin Dosso da ke kudu maso yammacin kasar. Hukumar ta kama manyan kulli 400 na tabar wiwi da kwayar diazepam kati 200 da sauran kwayoyi masu yin illa ga kwakwalwa. Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce tun a farkon watan Afrilu ta yi kamun kayayyakin a kauyen Gatawani amma sai yanzu ta yi holen su sannan aka mika su ga gwamnati. Wannan kamun na zuwa ne bayan kame-kame da dama da hukumar ta yi a makonnin da suka gabata a kan iyakar Jamhuriyar Benin da Nijeriya. A karshen watan Maris, hukumar ta kwastam ta kama manya-manyan dauri 18 na tabar wiwi wadanda kudinsu ya kai kimanin CFA miliyan tara a kauyen Indo da ke kusa da Kogin Neja. Kafin nan kuma, hukumar ta kama dauri 12 na tabar wiwi da nauyinsu ya kai kilo 7.75 wadanda suke cikin jaka. Gabanin haka, a ranar 27 ga watan Fabrairu hukumar ta yi wawan kamu da hadin gwiwar ‘yan sanda a Sabon Birni inda ta kama wata mota dauke da dauri 69 na tabar wiwi. Yankin sahel dai na daga cikin wuraren da ke fama da rashin tsaro a Afirka. Haka kuma rahotannin da ake samu na kai samame ga maboyar ‘yan bindiga na nuna cewa ana samun miyagun kwayoyi wadanda ‘yan bindigar ke amfani da su. Hukumomi musamman a yankin na sahel na ganin yaki da miyagun kwayoyi yana daga cikin hanyoyin yaki da ta’addanci.