Mutum miliyan 1.3 ne suka je Umara Saudiyya

0
263

Ministan aikin Hajji da Umara Dakta Tawfiq Al-Rabiah ya ce biranen Makka da Madina sun samu masu ziyarar ibada daga ƙasashen waje masu yawan gaske a wannan wata.

Dakta Tawfiq ya ce ya zuwa yanzu an samu masu ziyarar ibada miliyan 1.3 a manyan biranen ƙasar biyu.

Ministan ya ce ana samun ci gaba a harkokin sufurin masu ziyarar ibada tare da inganta harkokin ibada musamman a cikin masallatai biyu masu alfarma a ƙasar.

”Muna bakin ƙoƙarinmu wajen samar da kyakkyawan yanayi domin jin daɗin mahajjata a biranen Makka da Madina”, in ji shi.

”A kodayaushe muna kan inganta biranen biyu, kuma akwai wuraren tarihi sama da 100 tsakanin biranen biyu”, a cewarsa.

Ministan ya ce ana sa ran sama da mutum miliyan biyu ne za su yi aikin hajjin bana a wannan shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here