Yadda ɗaya daga cikin ƙasashe mafi wayewa a duniya ta faɗa cikin bala’i

0
100

Yayin da kogin Tigris yake bi ta Babban Birnin Bagadaza, yana cike da sirruka da dama. Babu wanda ya san adadin gawarwakin da aka jefa ciki. Shekara ashirin bayan mamayar da Amurka ta jagoranta, har yanzu abu ne mai wuya amincewa da yadda ɗaya daga cikin mafi kyawun wayewa, daɗaɗɗen garin Babylon ya faɗa cikin irin wannan bala’i.

A yanzu, duk da irin daidaiton da aka samu, har yanzu ana danganta Iraki da kashe-kashen ramuwar gayya na masu kishin addini da motoci maƙare da bam da ɓullar mayaƙa ƴan Sunni da ƴan Shi’a masu tsattsauran ra’ayin Musulunci. Wasu daga cikin tushen sun samo asali ne a farkon shekarun 2000, lokacin ikon Amurka da ba shi da na biyu.

Matakin kai mamaya

Ƙungiyar ƴan tawaye ta Al-Qaeda ta sha kai wa Amurka hari a ƙasarta da hare-haren 9 ga watan Satumba.

Amurka ta tsara wani ƙawance domin kai mamaya Afghanistan, cibiyar al-Qaeda a 2001.

hannun abin da aka zo ana kira IS.

Da alama sojojin Iraki sun ɓace. “Sojojin da aka gina cikin shekara 10, sun ɓace a sa’oi 10,” in ji tsohon shugaban Ƙurdawa Massoud Barzani.

Tsohon Firaminista al-Maliki yana mamakin yadda kwamandojin rundunonin sojin suka iya janyewa ƴan sa’oi kafin nausawa IS. Haider al-Abadi ya maye gurbin al-Maliki a matsayin Firaminista kuma ya fi fito da matsalolin.

“Ya kasance wani faɗan ɓangaranci wanda ya zama babbar matsala,” in ji shi. “IS ta zama ta ɓangaranci amma tsarin ƙasar shi ma yana nuna ɓangaranci.”

Sai dai al-Abadi ya ƙi bayyana tsare-tsaren al-Maliki a matsayin na ɓangaranci kuma yana da nasa bayanan kan dalilin da ya sa wasu biranen ƴan Sunni suka yi maraba da IS.

“Akwai cin hanci a tsarin tsaron ƙasar,” in ji shi. “Ƴan Iraki sun rasa ƙwarin gwiwa a kai kuma a shirye suke su ha da kai da sauran domin kare kansa.”

Wani gagarumin yunƙurin jami’an tsaron Iraki sun taimaka wajen murƙushe IS bayan shekara huɗu. Amma yaƙin ya bar baya da ƙura a Lardunan Sunni. An ga hakan a Mosul, birnin ƴan Sunni mafi muhimmanci.

Da alamar tausayi a muryarsa, malamin da ke ɗaya daga cikin daɗaɗɗun masallatan Mosul ya buƙaci a maido da tsarin baya sannan Iraki ta koma hannun wani kamar Saddam Hussein. Ya buƙaci a ɓoye sunansa.

“Ba mu datacewa a kan abin da ke faruwa a ƙasar nan,” kamar yadda ya ce. “Amurka ta ce ta ƴantar da Iraki amma ta miƙa ƙasar ga Iran cikin sauƙi.”

Amma wa ke da iko kan muhawarar malamai a lokacin da ake fafutukar inganta rayuwa. Al’ummar Iraki matasa ne da ba su da aikin yi.

Idan Iraki ta zama ƙasar da ke samun arzikin ƙasar, ku yi tunanin abin da wannan ƙasar mai tarin arzikin albarkatun ƙasa za ta iya cimma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here