Home Labarai Abin da wasu malaman addinai suka ce kan kiran Sarkin Musulmi na...

Abin da wasu malaman addinai suka ce kan kiran Sarkin Musulmi na daina kalaman kiyayya a Najeriya

0
229

A sakonsa na taya al’ummar Kiristocin kasar bikin Easter a ranar Litinin Sarkin Musulmin ya nemi hadin kan shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, Daniel Okoh, don kira ga malaman addinai da su kaurace wa kalaman siyasa a wuraren ibada.

“A matsayinmu na al’umma daya da muka hadu ta wajen babanmu Annabi Ibrahim, abubuwan da ke faruwa na al’amuran siyasa a baya bayan nan a kasarmu abar sonmu na yi wa al’ummominmu barazana sosai,” in ji Sarkin Musulmin.

Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda shi ne shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci a Najeriya NSCIA, ya ce akwai bukatar Kungiyar CAN da ta NSCIA su yi aiki tare don tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.

Me malaman addinai suka ce?

Rabaran Joseph Hayab, Shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN reshen jihar Kaduna, ya shaida wa TRT Afrika cewa wannan kira ya zo a daidai, “duba da yadda lamuran masu wa’azi a majami’u da masallatai suke janyo ce-ce-ku-ce.”

Rabaran Hayab ya ce, “Ina zaton Sultan ya yi wannan kira ne sakamakon karuwar zaman dar-dar a kasar kafin da kuma bayan zabukan da suka gabata, inda wasu limaman suka yi amfani da mumbarinsu wajen tallata ‘yan takara”.

A nasa bangaren Sheik Muhammad Bin Uthman, babban limamin Masallacin Sahaba da ke Kano ya ce, “Amfani da mumbari a wasu lokutan ka iya nufin yada zantukan kage da cin zarafi. To ya kamata a jawo hankalin irin limaman da ke yin haka.”

“Sai dai kuma kasancewar akwai malamai ‘yan siyasa, tun da har gwamna an samu wanda limami ne a wajen ibada a Nijeriya, zai yi wuya a raba irin wadannan malamai da yin sharhi kan matsalar al’ummarsu da ta shafi siyasa yayin da suke wa’azi,” kamar yadda malamin ya gaya wa TRT Afrika.

“Amma dai maganar kiyayya kwata-kwata bai dace a kawo ta kan mumbari ba”.

Shi ma Rabaran Hayab ya jaddada cewa, “Babu batun kalaman kiyayya a littafi mai tsarki na Baibul.

“Yesu ya yi kira ga sahabbansa da cewa duk wanda ya ce wa dan uwansa ‘wawa’, to za a yi masa hisabi”.

Duka malaman biyu sun jaddada cewa akwai bukatar a yi amfani da mumbari wajen yada manufofin adalci da girmama juna da zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

X whatsapp