Dabarun da Manchester City ta bi wajen lallasa Bayern a wasan kofin Zakarun Turai

0
193

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta lallasa kungiyar Bayern Munich da ci uku rigis a daren Talata, yayin fafatawar zangon farko na wasan kusa da na karshe a kofin Zakarun Turai.

Wasan ya gudana ne a gidan City da ke filin wasa na Etihad Stadium a Ingila.

Dan wasan tsakiya na City, Rodri, shi ya fara zura kwallo a minti na 27 da soma wasan, sannan Bernardo Silva ya aika ta biyu a minti na 70.

A daidai minti 76 na wasan, sai zakakurin dan wasan nan Erling Haaland ya aika tasa kwallon, wadda da ita ya kafa sabon tarihi na dan wasan da ya fi zura kwallaye a Ingila, cikin kaka guda a duka gasanni.

Hakan ya tabbata ne sakamakon tunkude dan wasan Liverpool, Mohamed Salah daga wannan mukami, wanda ya taba zura kwallaye har 44 a kakar 2017/18.

Wannan wasa ya nuna fifikon kocin City, Pep Gaurdiola wanda ya samu nasara a karo na bakwai na haduwarsu da Thomas Tuchel, wanda bai yi wata guda da karbar ragamar jagorancin kungiyar Bayern ba.

Tun da fari, masu sharhi kan wasan na Talata, suna ganin mai horar da Bayern, wato Tuchel ya tafka kurakurai, kamar ajiye Thomas Muller da Sadio Mane a benci har sai wajen karshen wasan.

Haka ya faru duk kuwa da cewa akwai ‘yan wasa irin su Serge Gnabry, da Kinsley Coman, da Upamecano, wadanda ba su taka rawar gani ba.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, an yi tsammanin Tuchel zai sako gwarazan nasa. Amma sai ya bari har sai da aka ci su kwallaye uku, sannan ya sako dan wasan gaba Muller ya cire Gnabry, sannan mai tsaron baya Joao Cancelo ya maye gurbin Alponso Davies.

Masu fashin bakin sun kara nuna rashin azancin Tuchel wajen zabin cire Jamal Musiala don ya sako Sadio Mane a minti na 70.

Hasali ma, mai tsaron ragar Bayern, Sommer shi ake ganin ya ceto kungiyar daga karin kwallaye, sakamakon bajintar da ya nuna wajen tare kwallo sau da dama a tsawon wasan.

A bangaren Guardiola, canji daya kawai ya yi inda ya cire Kevin De Bruyne ya sako Julian Alvarez a minti na 68.

Ganin yadda Tuchel ya gaza dinke barakar Bayern har ta kai ga an zura mata kwallaye uku a zangon wasan na farko, ana ganin tamkar kungiyar City ta haye zuwa wasan daf da na karshe ne.

Zuwa yanzu, bayan da Tuchel ya jagoranci wasannin da ba su fi biyar ba a matsayin sabon kociyan Bayern, tuni wasu masoya kulob din suka fara kewar tsohon kociyansu da aka sallama don a kawo Tuchel din, wato Julian Negelsmann.

A wani bangaren na wannan zagaye na kusa da na karshe a kofin Zakarun Turai, kungiyar Inter ta Italiya ta doke SL Benfica ta Portugal, da ci biyu da nema.

Yanzu dai Tuchel da kulob dinsa na Bayern suna da damar warware wannan sarkakiya a sati mai zuwa, yayin da za su karbi bakuncin kulob din na City, don ramakon zango na biyu na wasan da za a buga a Allianz Arena ranar Talata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here