Jamus ta kori jakadar Chadi daga kasarta

0
159

Kasar Jamus ta dauki wani mataki mai kama da ramuwar gayya inda ta bukaci jakadar Chadi a kasarta ta fice daga Berlin cikin sa’o’i 48, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Chadi ta sanar a ranar Talata.

Wannan matakin ya zo daidai da wanda kasar Chadi da ke yammacin Afirka ta dauka a makon jiya.

“Domin mayar da martani kan kora mara amfani da aka yi wa jakadanmu a Chadi, a yau mun kira jakadar Chadi a Berlin, Miriam Ali Moussa inda muka bukaci ta bar Jamus cikin sa’o’i 48.

Muna sane cewa lamarin zai zo ga haka,”kamar yadda ma’aikatar ta wallafa a shafinta na Twitter.

 

A makon jiya ne aka kori jakadan Jamus a Chadi, Gordon Kricke, inda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce an dauki matakin ne sakamakon “saba ka’idoji da kuma rashin da’a ga harkokin diflomasiyya’.

Wasu jami’an gwamnatin Chadi sun ce an kori Mista Kricke ne saboda suka da yake yi kan jinkirin gudanar da zabe da kuma matakin kotu na barin shugaban soji na riko Mahamat Idriss Deby ya yi takara.

Sai dai ma’aikatar harkokin wajen Jamus ta bayyana cewa Mista Kricke ya gudanar da aikinsa ne yadda ya kamata kuma ya yi aiki ne domin kare hakkin bil adama da kuma ganin an samu sauyi zuwa gwamnatin dimokradiyya cikin sauri.

Ana ganin wadannan matakai da kasashen suka dauka za su iya tasiri ta fuskar diflomasiyya a tsakaninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here