Jamus za ta halasta shan tabar wiwi ‘don amfanin kai’

0
262

Gwamnatin hadaka ta Jamus karkashin jagorancin Firaminista Scholz ta sanar da cewa za ta samar da sabuwar dokar bai wa mutane damar mallakar giram 25 na tabar wiwi don amfanin kai.

A lokacin da yake magana a wajen taron manema labarai, Ministan Lafiya na Jamus Karl Lauterbch ya ce manufar wannan doka ita ce a rage kasuwancin tabar wiwi a kasuwannin bayan fage da kuma rage yawan aikata muggan laifuka.

Ya ce, “Dokar mallakar tabar wiwi ta ba taba yin nasara ba,” inda ya kara da cewa hana mallakar tata gaba daya bai hana amfani da ita ba ko kuma hana ta shiga hannun bata-gari ba.

Ya ce “Sabuwar dokarmu ta shafi kula da rarraba tabar wiwi a tsakanin balagaggu kuma a takaice”.

Sabon kudirin dokar da gwamnati ta fitar ya bayyana masu shekara 18 zuwa sama za su iya mallakar tabar wiwi da ba ta wuce yawan giram 25 ba.

Za kuma a bayar da dama ga wadanda za su noma zangarniya uku kawai don amfanin kai.

Kungiyoyin da ba na kasuwanci ba da suke da mambobin da ba su wuce 500 ba ma za su samu izinin rarraba wa mambobinsu tabar wiwi din.

Kowanne mamba zai iya samun giram 50 na tabar a kowanne wata.

A makonni masu zuwa gwamnatin Olaf Scholz ta hadaka take shirin kammala wannan doka tare da fara aiki da ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here