Rashford ba zai yi wa United wasu wasannin ba

0
155

Marcus Rashford ba zai buga wa Manchester United wasu wasannin ba, sakamakon jinya da zai yi.

Mai shekara 25 dan kwallon tawagar Ingila ya ji rauni ranar Asabar a karawar da United ta ci Everton a wasan Premier League.

United ba ta fayyace kwanakin da zai yi jinya ba, illa ta ce zai murmure ya buga mata tamaula kafin karshen kakar nan.

Rashford mai kwallo 28 a bana ya buga wa United dukkan karawar lik a 2022/23.

United za ta karbi bakuncin Sevilla a wasan farko a quarter final ranar Alhamis a Europa League a Old Trafford.

An canja da wasan a minti na 80 ranar Asabar, bayan da United ta doke Everton 2-0 a Old Trafford, yana fita daga fili ya wuce dakin hutun ‘yan wasa.

Za a ci gaba da auna koshin lafiyar dan kwallon a lokacin da yake jinya, wanda ake fatan zai ci gaba da taka leda kafin a karkare kakar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here