Yadda jami’an tsaro suka tsare Peter Obi a London

0
107

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar LP ya ce jami’ai sun tsare tare da hantarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi a birnin London.

Mai magana da yawun kwamitin kamfe na jam’iyyar LP, Diran Onifade ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a filin jirgin sama na Heathrow da ke London.

Ta ƙara da cewa jami’an shige da fice na Birtaniya ɗin ne suka titsiye tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar.

Diran Onafide ya ce hukumomi a Birtaniya sun tsare tare da yin tambayoyi ga tsohon gwamnan na jihar Anambra kan wani lamari da ya shafi wani mutum da ke yin sojan-gona da suna Peter Obi.

Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an sun sassauta wa Petetr Obi ne bayan wasu ƴan Najeriya da ke a filin jirgin sun sanya baki.

Peter Obi dai ya isa birnin na London ne domin bukukuwan Easter na mabiya addinin Kirista.

Bayanin ya nuna cewa bayan saukar Peter Obi a filin jirgin na Heathrow da ke London, jami’an tsaro sun zo wurin sa a lokacin da yake kan layin tantancewa, tare da miƙa masa wata takarda da ke ƙunshe da umurnin tsarewa, sannan suka buƙace shi da ya fita daga layi.

Onifande ya ce jami’an sun yi wa Peter Obi tambayoyi na tsawon lokaci, wanda abu ne da ba a saba ganin ya faru ga wani mutum da ya kwashe sama da shekara 10 yana rayuwa a ƙasar ba.

Sai dai mutane ƴan asalin Najeriya sun rinƙa ɗaga muryoyinsu domin sanin dalilin da ya sa aka tsare tsohon gwamnan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here