Zababben dan majalisa mai wakiltar Chibok ya rasu

0
146

Zababben Dan Majalisar Dokokin Jihar Borno Mai Wakiltar Mazabar Chibok, Nuhu Clark, ya rasu sati bakwai cif kafin ranstar da shi.

Rahotanni daga jihar sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne a kasar Indiya ranar Litinin, yayin da ake jinya.

Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Yada Labarai da Al’adu na jihar, Babakura Abba Jatau, ya tabbatar da rasuwar Clark a yayin wata hira da manema labarai a Maiduguri, ranar Laraba.

Abba Jatau ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar za ta bayar da sanarwa a hukumance bayan tattaunawa da iyalan marigayin.

Kwamishinan ya kuma jajanta wa iyalan marigayin inda ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi, ba a gare su kadai ba, har ga daukacin mutanen Kudancin Borno da ma jihar baki daya.

Da ya ke nuna alhininsa bisa rasuwar, Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Umar Kadafur, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga Jam’iyyar APC bisa la’akari da irin gudunmawar da marigayin ya bayar wajen ci gaban jihar.

Marigayi Clark shi ne Kwamishinan Yaki da Fatara na Jihar Borno kafin ya yi murabus a ranar 25 ga Afrilu, 2022, domin tsayawa takarar dan majalisar jiha mai wakiltar mazabarsa ta Chibok a karkashin jam’iyyar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here