Gwamnatin Kamaru ta sake gina gadar da Boko Haram ta tarwatsa

0
105

Gwamnatin Kamaru ta kaddamar da sabuwar gadar da ke bai wa mazauna yankin arewacin kasar damar tsallakawa zuwa yankin Arewa maso gabashin Najeriya, wadda aka sake ginawa bayan da ‘yan Boko Haram suka tarwatsa ta a 2015.

sauran ma’aikata kaurace wa aikin saboda hare-hare.

Majiyoyi sun ce bayan kammala aikin wanda aka kaddamar a ranar Litinin da ta gabata, an kara adadin jami’an tsaro domin bai wa matafiya kariya a yankin, yayin da a hannu daya bayanai ke cewa kafin rusa wannan gada a shekara ta 2015, kowacce shekara gwamnatin Kamaru tana samun abin da ya zarta Dalar Amurka milyan 16 a matsayin kudaden shiga.

Ko baya ga ‘yan kasuwa daga Najeriya da kuma Kamaru, dubban matafiya ciki har da ‘yan kasuwa daga Chadi ne ke amfani da wannan gada da ake kira ‘’Gadar Mayo-Lamini. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here