‘Yan kungiyar asiri sun yanke kan dan sanda, sun jefa gangar jikinsa a rijiya

0
133

Rundunar ‘yan  sandanJihar Akwa Ibom, ta fara binciken kisan gillar da ake zargin wasu ‘yan kungiyar asiri suka yi wa daya daga cikin jami’anta mai suna Uwem Cletus, da ke aiki a yankin Ikot Abasi Akpan a karamar hukumar Mkpat Enin a jihar.

Leadership ta ruwaito cewa, marigayi Cletus na aikinsa a Mkpat Enin, inda ayyukan ‘yan kungiyar asiri ya yi kamari da sace mutane da yin fashi da makami da aikata sauran manyan laifuka.

‘Yan kungiyar sun kama marigayin ne sannan suka yanke kansa suka kuma jefa gangar jikinsa cikin wata rijiya.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Odiko Macdon ya shaida wa manema labarai cewa, kwamishinan ‘yansandan jihar Olatoye Durosinmi, ya nuna damuwarsa kan aukuwar lamarin, inda kuma ya umarci jami’ansa da su bazama don farautar wadanda suka aikata laifin.

Ya ce, marigayi Uwem Cletus ya kasance daya daga cikin ‘yan kwastanbulari na musamman, inda ya ce, sun samu rahoton farko na bacewarsa, inda rundunar ta tura jami’anta nemansa.

A cewarsa, a yayin bincike sun bankado cewa an yanke masa kai an kuma jefa gangar jikinsa cikin rijiya.

Ya ce, “Ba za mu rike hannu mu bar wannan lamarin ya tafi a haka ba, inda kuma ya mika ta’aziyarsa ga ‘yan uwa da abokan arzikin mamacin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here