Jami’an ‘yansandan caji ofis din Apo sun samu nasarar dakile wani yunkurin fashi da makami tare da cafke wasu da ake zargi da hannu a lamarin biyo bayan kiran gaggawa da suka samu.
Jami’ar watsa labarai na hukumar ‘yansandan Nijeriya reshen birnin tarayya FCT, SP Josephine Adeh, ta ce, wajajen karfe 6 na safiyar ranar Laraba ne ‘yansandan caji ofis din Apo suka samu kiran gaggawa kuma cikin hanzari suka dauki matakin gaggawa.
Ta ce, lokacin da ‘yan fashin suka hango tawagar ‘yansanda, sun arce suka bar wata mota mai lauyin ash kirar BMW mai dauke da lamba ABJ 440 KX inda suka samu na’urar laptop guda biyu da tv na kallo plasma guda uku a cikin motar da ake tunanin fashinsu suka yi a wani wurin na daban.
“Kazalika an hango wata mota kirar Volkswagen Golf mai lamba LUY 899 KV yayin da ta gudu lokacin da ‘yansandan suka iso.
“Jami’anmu sun bi sawun motar kuma an cafketa a wajen shatale-talen Games Village. Daga baya an gano matukin motar da suna Dahiru Mu’azu da wani mutum mai suna Halifa Hamisu dukka an kamasu.
“Da wadanda aka kama ake zargin da kayan da aka samu dukka suna hannun ‘yansanda inda bincike ke cigaba da gudana domin kamo sauran wadanda suka gudun,” a cewar SP Adeh.
A cewarta za su gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotun da zarar aka kammala bincike.
Kazalika, ‘yansandan sun nemi hadin kai jama’a a kowani lokaci tare da ce suke sanar musu da dukkanin wani motsin wadanda ba su gamsu da takunsu ba domin daukan matakin gaggawa.
Hukumar ta bayar da lambobin da jama’a za su ke kiran gaggawa idan bukatar hakan ta taso: 08032003913, 08061581938, 07057337653, and 08028940883, yayin da kuma jama’a za su ke shigar da korafe-korafen idan suna da shi ta lambar 0902 222 2352.