Zakarun Turai: Milan ta sake doke Napoli, bayan lallasa ta da 4-0 a Seria A

0
147

A farkon wasan dai Napoli ce ta dukufa wajen kai wa AC Milan hare-hare, amma daga bisani labari ya sauya.

Karo na biyu kenan da Milan ke doke abokiyar hamayyar tata, domin kuwa kwanaki 11 da suka gabata, Napolin ta  sha kashi da kwallaye 4-0 a karawar  da suka  yi a gasar Seria A.

Napoli wadda a yanzu haka ke jagorantar teburin gasar Seria A da maki 74, ta buga dukkanin wasannin biyu na baya bayan nan ne ba tare da tauraronta ba Victor Osimhen dan Najeriya, wanda ya ci wa kungiyar ta sa kwallaye 25 a dukkanin wasannin da ya buga mata a kakar wasa ta bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here