Halin da ake ciki kan ceto ƴan matan Chibok

0
72
ISWAP BOKO HARAM
Boko Haram ISWAP

A cikin bayanin da ta fitar, ƙungiyar BBOG ta bayar da alƙaluma waɗanda ta ce su ne bayani na baya-bayan nan game da halin da yaran makarantar ta Chibok suke ciki tun bayan sace su a 2014.

  • Yawan ɗaliban da aka sace: 276
  • Yawan ɗaliban da suka tsere daga hannun mayaƙa: 57
  • Yawan ɗaliban da mayaƙan suka saki: 107
  • Yawan ɗaliban da sojoji suka ceto: 16
  • Yawan ɗaliban da har yanzu ba a san inda suke ba: 96

Ci gaba da garkuwa da mutane

Najeriya dai na ci gaba da fuskantar rikice-rikice na masu riƙe da makamai da kuma masu iƙirarin jihadi.

A tsakanin 2020 zuwa 2021 an samu rahotannin jerin munanan garkuwa da mutane a ƙasar, ciki har da waɗanda aka yi a makarantu.

Kamar na makarantar sakandaren Ƙanƙara da ke jihar Katsina, da na Kagara a jihar Neja, da Jangebe a jihar Zamfara, da Tegina a jihar Neja da kuma Yawuri a jihar Kebbi.

Irin waɗannan hare-hare sun tursasa rufe makarantu a jihohi da dama, musamman a arewacin ƙasar.

Amnesty International ta buƙaci gwamnatin Najeriya ta ɗauki ƙwararan matakai wajen ganin ta kawar da ayyukan ƙungiyoyin ƴan bindiga irin su Boko Haram da ƴan fashin daji daga ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here