Lauyoyin mawaki Rarara sun bayyana a gaban kotu

0
668

Lauyoyin Kahutu Rarara sun bayyana a gaban kotun shari’ar musulunci da ke rijiyar zaki.

Idan za ku iya tunawa wani dan kasuwa ne ya yi karar mawakin bisa cewa yana binsa Naira miliyan goma na wayoyin da yake karba yana rabawa mutane.

A zaman  da ya gabata dai kotun ta bayyana yadda mawakin ko lauyoyin sa suka gaza amsa sammacinta.

Amma a Alhamis din nan lauyoyin sun bayyana a karkashin Barista G.A Badawi inda ya bukaci a basu dama sui nazarin tuhume-tuhumen da ake yi wa mawakin, domin su samu samar mahar da martani.

Kotun ta sanya ranar Litinin 17 ga Afrilun da muke ciki domin ci gaba da shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here