An aike da direba gidan yari kan cizon yatsan dan sanda a Ghana

0
129

Wata kotu a gundumar Assin-Fosu da ke Ghana ta aika da wani direban motar haya kurkuku bisa samunsa da laifin cizon yatsan dan sanda a yunkurinsa na hana a kama shi.

Kamfanin watsa labarai na kasar Ghana GBC ya ruwaito cewa Ebenezer Nkoom, dan shekara 24, ya amsa laifuka 13 da ake zarginsa da aikatawa ciki har da cutarwa da kin yarda a kama shi da saba wa dokoki bakwai na amfani da titi.

Mai shigar da kara Gilbert Ayongo ya shaida wa kotu cewa wanda aka kama da laifin ya tsaya da motarsa a wani wuri da bai kamata ba domin daukar fasinja ba tare da la’akari da cewa ya shiga hakkin wasu ba.

Sai ‘yan sanda suka same shi suka shaida masa cewa ya daina tsayawa wurin daukar fasinja amma sai ya kafe kan cewa ba zai daina tsayawa wurin ba har sai ‘yan sanda sun kama duka sauran direbobin da ke yin haka, a cewar Gilbert.

Ya bayyana cewa ba a wuce sa’a daya da yin haka ba sai direban ya dawo wurin domin sake daukar fasinja wanda hakan ya sa aka kama shi, inda ‘yan sanda suka shiga motar shi domin zuwa ofishin ‘yan sanda.

“ A kan haka ne ya tafi da su zuwa wani wuri domin ya gudu, a kokarin sake kama shi sai ya ciji yatsan konstable Ayamba inda ya ji masa ciwo a yatsan sa,” in ji shi.

Daga nan ne wani mai mota wanda ya shaida lamarin ya yi sauri ya dauki dan sandan da aka ji wa ciwo sa’annan ya bi mai laifin wanda ya je ya ajiye motarsa a kusa da wani daji ya gudu.

Gilbert ya bayyana cewa bayan sa’o’i biyu an gano Ebenezer inda aka kama shi. Bayan binciken da aka gudanar, an gano cewa direban ya ki sabunta lasisin tukinsa kuma yana tuki babu safaya taya a cikin motarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here