Wata budurwa wanda ba a bayyana sunanta ba ta ce da zarar ta kammala sahur sai ta sha Kodin kwalba daya kafin ta iya yin azumin ranar.
” Bayan na gama cin duk abinda zan ci da asuba, sai kuma na rungumi kwalbar Kodin dina in kwankwada. Idan na fara barci sai an kusa yin bude baki. Hakan yana sa bana jin Azumin.
Wani matashi cewa yayi tunda aka fara Azumi ya ajiye shaye shaye sai bayan Ramadana.
” Na yi haka ne domin in samu damar samun lokaci da maida hankali wajen yin bauta.
” Amma akwai abokai na wanda su da ganyen wiwi suke bude baki. Da zaran ladan ya yi kira sallar magariba, wato bude baki, za su yi wa mandular wiwi wuta, ita ce dabinon su, kafin daga baya sai kuma a nemi abin sha ko ci.
Da yawa daga cinkin matasa sun rungumi shaye-shayen muggan kwayoyi, ta yadda kamar ba su iya rayuwa babu su.
Abin tashin hankali game da wannan al’amari shine yadda mata suka dulmiya cikin harkar shaye-shaye tsundum, suna kan-kan-kan da maza a harkar. Ba taba sigari ba, Wiwin ne, SK ne, Shisha ne, koken ne, zakami, kwata, Omo, Fetur, Kashin Kadangare, kalanzir, Kodin, giya, burkutu, fito, bammi, Kain Kain, Roci, tramadol, duk wanda suka ci karo da, afkawa kawai suke, wasu da shi suke buda baki wasu kuma sahur, wasu kuma sun zabi wasu sun ajiye wasu sai bayan sallah.