An tsinci gawar wani almajiri a Jigawa babu ido

0
134

Rundunar ƴan sanda a jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani almajiri ɗan shekara 16 bayan an tsinci gawarsa a wani daji kusa da ƙaramar hukumar Kiyawa da ke jihar.

A cikin wata sanarwa mai magana da yawun ƴan sandan jihar DSP Lawal Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an cire ɗaya daga cikin idanun almajirin.

Shiisu ya ce Malamin marigayin, Malam Mustafa da ke garin Shuwarin, shi ya kai wa jami’an tsaro rahoto kan lamarin da ya faru.

DSP Shiisu, ya ce Malamin ya kai korafin cewa ɗaya daga cikin ɗalibansa mai suna Yusufa Mustapha ɗan shekara 16, ya shiga daji don neman itace da misalin ƙarfe 8 na safe, wanda kuma daga nan ne ba su ji ɗuriyarsa ba sai dai ganin gawarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here