Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nemi afuwar Kanawa da su yafe masa duk abin da ya yi musu ba daidai ba a yayin da wa’adin mulkinsa ya taho gangara.
Ganduje ya yi wannan kira ne yayin da ya halarci Tafsirin Al-Qurani mai girma a Masallacin Juma’a na Al-Furqan da ke titin Alu a birnin Dabo.
A cewar Ganduje, kwanaki kalilan suka rage masa ya sauka daga mulki a matsayinsa na gwamnan jihar, saboda haka ya ga dacewar ya nemi gafarar duk wadanda ya jagoranta.
Ya ce shi dai a bangarensa ya yafe wa duk wani wanda ya yi masa ba daidai walau ya sani ko kuma akasin haka, saboda haka shi ma yana bukatar da a yafe, kowa ya yafi juna.
“A yanzu zan iya cewa wa’adin mulkina ya zo karshe a matsayin Gwamnan Kano.
“Ina mai yin bankwana tare da yi wa kowa fatan alheri a rayuwa.
“Dangane da wadanda na yi wa ba daidai, Limami ya riga da yin wa’azi kan muhimmancin yafiya.
Duk wani ba daidai walau na lafazi ne ko a aikace da wani ya yi a kaina, na yafe wa kowa.
“Ni ma ina rokon da a yafe min, duk mu yafi juna. Na gode,” a cewar Ganduje.
A wani tafsirin da ya halarta na Sheikh Nasidi Abubakar Goron Dutse, Ganduje ya ce ya shafe shekaru 6 a matsayin Kwamishina a Kano, shekara 8 a matsayin Mataimakin Gwamnan sannan kuma da shekara 8 a matsayin Gwamnan Kano.
“Dole ne na soma da yi wa Allah godiya da wannan dama da ya ba ni.
“Amma kuma a tsawon wannan lokaci, dole ne akwai wurare ko lokutan da na yi daidai da kuma wadanda na yi akasin haka.
“A wasu lokutan ma wani ne zai aikata ba daidai ba a madadinka, saboda haka duk wadanda na sabawa, ina rokon da su yafe min.”
Yadda wasu suka yi wa Ganduje martani
Sai dai bayan bayyanar wadanda bidiyo guda biyu mabanbanta da aka nadi Ganduje yana neman gafara, ma’abota dandalan sada zumunta daga ciki da wajen Kano sun mayar da martani, inda kowanne yake bayyana irin nasa ra’ayin.
yayin da an samu wadanda suka ce su tuni sun yafe tare da yaba wa gwamnan da ya fito bainar jama’a yana neman gafara, an kuma samu wadanda suka gindaya wa gwamnan sharadin da har sai ya cika sannan za su yafe masa.
Haka kuma, an samu masu cewa a kai kasuwa domin kuwa ba za su yafe ba.
Wani Mas’ud Abdulhamid cewa ya yi, “mun yafe maka mai girma gwamna, Allah Ya yafe mana baki daya.”
Shi kuwa a cewar Reedwan Shagari, “Kanawa za su yi kewar gwamna nagari mai kirki.
“Ganduje ne ya nuna dattako duk da irin zagon kasa da mutane suka rika yi masa, amma ko kadan bai damu.”
Wani mai suna Yakuba Magaji Mani ya ce, “Ina malaminmu Abduljabbar? Ka sako mana shi idan har kana son mu yafe maka.”
“Mun yafe maka Baba. Allah Ya kara inganta lafiyarka,” a cewar Mustapha Idris Abdullahi.
Sai wani Mubarak Sani Lambu, inda ya ce “Don Allah Kanawa mu yafe wa Baba Ganduje mu manta sannan mu mayar da komai ba komai ba.”