Hukumar zaben Najeriya INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben Adamawa

0
90

Hukumar zaben Najeriya INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben gwamna a Jihar Adamawa.

Kwamishinan watsa labarai da wayar da kan jama’a na hukumar Festus Okoye ya sanar da hakan.

Sanarwar hukumar zaben ta biyo bayan ayyana Aisha Binani a matsayin gwamnan jihar Adamawa da kwamishinan zaben jihar Barrister Hudu Yunusa ya yi da safiyar Lahadi.

Sai dai a sanarwar da hukumar zaben ta fitar, ta yi watsi da sakamakon da Hudu ya sanar tare da nuna cewa ya kwace aikin baturen zaben jihar.

Haka kuma hukumar zaben ta gayyaci kwamishinan zaben jihar da sauran jami’an da ke da hannu a lamarin zuwa hedikwatar hukumar da ke Abuja nan take domin karin bayani.

Tun da farko dai an ga wani bidiyo yana yawo a shafukan sada zumunta mai cike da hayaniya inda kwamishinan zaben Jihar Adamawa Hudu Yunusa ya ayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaben.

Sai dai an ji jama’a suna nuna turjiiya da kuma tababa a cikin bidiyon wanda bai kai minti guda ba.

An dai gudanar da zabe a zagaye na biyu a Jihar Adamawa tsakanin gwamna mai ci a jihar Ahmadu Fintiri na Jam’iyyar PDP da kuma Aishatu Binani ta Jam’iyyar APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here