INEC ta gayyaci kwamishinan zaben Adamawa zuwa Abuja

0
88

Hukumar INEC ta gayyaci Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa zuwa Abuja bayan ta yi fatali da sakamakon zaben Gwamnan Adamawa da ya yi azarbabin sanarwa tun kafin a kammala tattara sakamakon zaben.

Hukumar ta dakatar da tattara sakamakon zaben, sannan ta bukaci kwamishinan zaben da jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Mohammed Mele, da sauran wadanda abin ya shafa su bayyana a hedikwatarta da ke Abuja domin tattaunawa kan wannan dambarwa.

INEC ta bayyana cewa sanar da sakamakon zaben ba hurumin Kwamishinan Zabe ba ne, na jami’in tattara sakamakon zabe ne.

Sanarwar da kwamishinan harkokin hulda da jama’a na INEC, Festus Okoye, ya fitar ta ce sanarwar da Kwamishinan Zaben, Hudu Yunus Ari ya yi ba ta da amfani ballantana tasiri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here