Arsenal na nazarin daukar karin ‘yan wasan gaba saboda gasar zakarun Turai

0
171

Kungiyar Arsenal ta fara nazari kan sabbin ‘yan wasan gaba da ta ke bukatar kulla yarjejeniya da su kafin shiga sabuwar kakar wasa.

A halin yanzu Arsenal ce ke jagorantar teburin gasar Premier Ingila da tazarar maki 4 tsakaninta da Manchester City.

‘Yan wasan da Arsenal ke zawarci kamar yadda wasu  majiyoyi suka ruwaito sun hada da Dominic Calvert-Lewin na kungiyar Everton da kuma Dusan Vlahovic na Juventus.

Matakin dai na da nasaba da shirin da kungiyar ta fara na tunkarar gasar cin kofin zakarun Turai da za ta buga a kakar wasa mai zuwa, gasar da Arsenal ta shafe shekaru ba tare da haskawa a cikinta ba.

Vlahovic dan kasar Serbia, wanda Arsenal ta dade tana neman sayensa ya zura kwallaye 11, ya kuma taimaka wajen jefa wasu hudu a wasanni 32 da ya buga a kakar wasa ta bana da ya bugawa Juventus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here