An kashe mutane da dama, an kone gidaje a rikicin makiyaya da manoma a Filato

0
242

Rahotanni sun ce an kashe mutane da dama tare da kone gidaje a wani rikicin da ya barke tsakanin makiyaya da manoma a yankin Mai Tumbi da ke karamar hukumar Mangu a Jihar Filato.

Wakilinmu ya ruwaito cewa rikicin ya faro ne tun a ranar Juma’a, kuma har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ana tsaka da yin sa.

Wani mazaunin garin Ibrahim Musa ya ce, “har yanzu rikicin na ci gaba da faruwa. Daruruwan mutane ne ke gudun hijira daga kauyen. Ba zan iya ba ku ainihin adadin mutanen da aka kashe ba amma an kashe da yawa. Sama da gidaje 100 ne aka kone.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya shaida wa manema labarai cewa an tura ‘yan sanda da rundunar ‘Operation Safe Haven (OPSH)’ da ke aiki da jami’an tsaro da dama domin tabbatar da zaman lafiya a jihar da dawo da doka da oda.

Ya ce, “Ba na son na ba ku bayanai masu karo da juna. An tura jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.”

Babban Darakta Janar na Hukumar Samar Da Zaman Lafiya ta Jihar Filato (PPBA), Joseph Lengmang, wanda ya yi Allah wadai da lamarin ya ce, “Mun yi matukar bakin ciki da yadda lamarin ya faru a karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato, inda rahotanni masu tayar da hankali suka nuna cewa matsalar tsaro ta tabarbare a yankin, wasu sassan yankin da suka yi sanadin mutuwar dimbin rayuka da dukiyoyi masu yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here