Rundunar ‘yan sanda ta rage mukamin insifekta zuwa sajent kan musguna wa farar hula

0
108

Rundunar ‘yansandan Nijeriya (NPF) ta rage mukamin wani jami’inta mai suna Adejoh Siaka daga Insifekta zuwa Sajent bayan kamasa balo-balo a wani faifayin bidiyo yana cin mutuncin wani direba a jihar Ribas.

A wata sanarwar da Kakakin hukumar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya ce, hakan ya biyo bayan korafe-korafen da aka shigar wanda aka gabatar da hujja mai karfi a faifayin bidiyo da ya yadu sosai a social media a ranar Lahadi 9 ga watan Afrilu, 2023 da ke nuna yadda dan sandan ya take dokar aiki da tsarin gudanar da aiki wajen musgunawar a Emouha da ke jihar Ribas.

Kazalika, wani dan sanda Sajent Ndiwa Kpuebari, da ya kasance a wajen da abun ya faru amma bai tabuka komai wajen hana wannan mummunar aika-aikar na tir da janyo abin kunyan ba, ya sha kakkausar gargadi da jan kunne.

Kazalika, wani jami’in kuma Insifekta Friday Obaka, da aka tuhuma kan laifin amma daga baya aka gano baya ma nan a wajen da abun ya faru, an sallameshi ba tare da wani sharadi ba bayan gano bai ma wajen da lamarin ya wakana.

Kazalika, rundunar ta kuma ce, dukkanin ‘yansandan uku an sauya musu wajen aiki daga Shalkwatar hukumar a Ribas zuwa wasu wuraren domin cigaba da gudanar da aikinsu.

Har-ila-yau, Insifekta-janar na hukumar ‘yansandan kasa ya gargadi jami’ansa da ke gudanar da aikinsu bisa kwarewa da bin dokoki da ka’idojin aiki a kowani lokaci tare da kare hakkokin fararen hula kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin kasa na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here