Za a kammala titin Kaduna zuwa Kano kafin Buhari ya sauka — Fashola

0
129

Gwamnatin Tarayya ta ce za a kammala aikin titin Kaduna, Zariya zuwa Kano kafin ranar 29 ga watan Mayu.

Ministan ayyuka da gidaje, Mista Babatunde Raji-Fashola (SAN), ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, yayin da ya ke ziyarar duba aikin babbar hanyar.

Bangaren babbar hanyar na daga cikin aikin da ya kai kilomita 375.4 daga Abuja-Kaduna-Zariya-Kano da aka bayar a lokacin mulkin Buhari na farko.

Ya ce za a kammala sashen kuma za a bude shi kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki a watan Mayu.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewa, aikin sake gina hanyar Abuja-Kaduna-Zariya-Kano ya kasu kashi uku.

Fashola ya ce yayin da aka kusa kammala kashi na biyu da na uku wanda ya kai kilomita 210, sashe na daya daga Abuja zuwa Kaduna za a bar wa gwamnati mai jiran gado.

“Sashe na daya (Abuja-Kaduna) zai wuce wa’adin mulkin wannan gwamnati, mun yi asara kusan shekara guda a 2022, saboda aikata laifuka da kuma hakkokin hanya,” in ji shi.

Fashola ya bayyana cewa batutuwan da suka kawo tsaikon aikin sun hada da sake gina gine-gine, da na’urorin lantarki, da kasuwanni.

“Abin da muke bukata shi ne mu hada kai da Ministan Babban Birnin Tarayya, gwamnatocin jihohin Neja da Kaduna, domin dakile ayyukan da suke tafiya cikin sauri da kwanciyar hankali,” in ji shi.

Haka zalika, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya bayyana cewa gadar Neja ta biyu ita ma ta kammala don kaddamar da aikinta.

Ya bayyana shi a matsayin aiki na uku da gwamnatin Buhari ta gada.

Gambari ya yaba wa shugaban kasa bisa yadda ya samar da ayyukan more rayuwa a fadin kasar nan.

Manajan Daraktan Hukumar Kula da Zuba Jari ta Nijeriya, Aminu Umar-Sadiq, ya ce suna da hannu wajen samar da wasu ayyuka.

Ya ce baya ga kudade, yana da muhimmanci a warware matsalolin da suka shafi hakkin hanya da kuma tsaro don ci gaba da ayyukan kamar yadda aka tsara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here