INEC ta bukaci a hukunta kwamishinan zaben jihar Adamawa

0
145

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta bukaci babban sufeto janar na ‘yan sanda, Alkali Usman Baba daya gaggauta kama tare da gurfanar da dakataccen kwamishinan zaben Jihar Adamawa Barista Hudu Yunusa Ari.

INEC ta nemi wannan bukata ne kan zargin kwamishinan zabe na jihar Adamawa Barista Hudu Yunusa Ari da taka doka na yin azarbabin bayyana wanda ya ci zaben gwamna a jihar.

INEC ta nemi wannan bukata ne cikin wata sanarwa bayan wani taron gaggawa da hukumar ta yi kan batun danbarwar zaben na Adamawa.

“Tuni an rubutawa babban sufeto janar kan ya gaggauta bincika tare da garfunar da kwamishin zaben Adamawa Barista Hudu Yunusa Ari.”

Haka zalika INEC ta bukaci babban sakataren gwamnati da ya duba halin da kwamishinan ya nuna don daukar matakin da ya dace.

Hukumar da bayyana cewa baturen zaben jihar ne yanzu yake da hurumin daukar matakai a hukumar.

Tuni dai INEC ta dakatar da Barista Hudu tare da gargadinsa daya guji zuwa kusa da ofishin hukumar.

Bayan bayyana ‘yar takarar jam’iyyar APC, Aishatu Binani a matsayin wadda ta lashe zaben jihar, INEC ta kammala tattara sakamakon zaben tare da bayyana gwamman Jihar, Ahmadu Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here