An ga watan Sallah a Najeriya

0
264

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya.

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce ganin jinjirin watan da aka yi a a kasar ya sanya ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu, 2023 ta zamo 1 ga watan Shawwal, 1444.

Kwamitin tantance ganin wata karkashin jagorancin Maigirma Wazirin Sakkwato Farfesa. Sambo Wali Junaidu ne ya jagoranci aikin tabbatar da ganin watan a bana.

Cikin sanarwar da ya yi Sarkin Musulmi ya ce “mun samu bayanai daga wurare daban-daban a Najeriya kuma mun zauna da masana domin tabbatar da ingancin waɗannan bayanan gabanin mu sanar da al’umma cewa an ga watan.

Domin haka gobe Juma’a 21 ga watan Afrilu 2023 ita ce 1 ga watan Shawwal 1444,” in ji Sarkin Musulmi.

Ya yi kira ga sauran musulmin ƙasar da su ajiye azumi domin an ga wata, su kuma yi shirin zuwa masallaci domin halartar Sallar Idi a wurare daban-daban.

Akasarin Musulmai a fadin duniya dai sun tashi da Azumin watan Ramadan ranar 23 ga watan Maris 2023.

Ya kuma yi addu’a kan Ubangiji ya karɓi ibadun da musulmi suka yi a faɗin duniya.

Sannan ya yi wa Najeriya addu’ar zaman lafiya da kuma rokon Allah Ya taimaki sabbin shugabannin da aka zaɓa a ƙasar kwanakin da suka gabata.

Saudiyya tuni ta sanar da ganin watan a garin garin Tumair wanda hakan ke nufin ranar Juma’a ne sallah. Ko da yake da farko sai da ta ba da sanarwar ba a ga watan ba a lardun gashin ƙasar.

A Iran kwamitin ganin watan ƙarƙashin jagorancin shugaban addini na ƙasar Ali Kamenei ya ce ba a ga watan ba, don haka sallah sai ranar Asabar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here