Akalla mutum biyu ne ake fargabar sun mutu bayan wani bene da ake aikin gina shi a unguwar Wuse da ke Abuja ya rushe.
Ginin dai wanda ke kan titin Ademola Adetokumbo ya fadi ne da tsakar ranar Laraba lokacin da ake tsaka da aiki gina shi.
Mutum biyar ne dai aka ceto da ransu, wasu biyu kuma sun ji munanan raunuka yayin da ake ci gaba da aikin ceto a wajen.
Rahotanni sun ce yanzu haka dai jami’an Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da na Hukumar Kashe Gobara ta Kasa da kuma sauran jami’an tsaro irin su ’yan sanda da Sibil Difens da sauran ’yan sa-kai ne suke aikin ceton.