Gidajen zamani na taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da zazzabin cizon sauro

0
159

Wani sabon nazari da aka wallafa a kwanan baya ya shaida mana cewa, a yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara, mai yiwuwa gidaje irin na zamani su taimaka wajen rage barazanar kamuwa da zazzabin cizon sauro da kananan yara suke fuskanta a wurin, maimakon gidajen ciyayi na gargajiya, indan aka hada da sauran matakai wajen kyautata yin rigakafin zazzabin cizon sauro a nan gaba.

Wata kungiyar nazari ta duniya karkashin shugabancin masanan jami’ar Oxford ta kasar Birtaniya ta tantance yawan bayanan da suka shafi yadda zazzabin cizon sauro yake yaduwa a gidaje dake Afirka. An samu wadannan bayanai ne daga nazarce-nazarce guda 29 da aka gudanar a kasashe 21 na Afirka daga shekarar 2008 zuwa 2015.

Bayanan sun nuna cewa, daga shekarar 2008 zuwa 2015, yawan kananan yara da suka kamu da zazzabin cizon sauro a wadannan kasashe ya ragu da kaso 9 cikin dari zuwa kaso 14 cikin dari. Duk da yawan dukiyoyin da iyalai suke da su, da kuma magungunan kashe kwari da ake amfani da shi, masu nazarin suna ganin cewa, akwai wata alaka a tsakanin yadda kananan yara suke rayuwa a gidajen zamani, da kuma raguwar yawan kananan yara da suke kamuwa da zazzabin cizon sauro a yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.

Masanan jami’ar Oxford sun yi bayani da cewa, gidaje masu inganci su kansu na iya hana sauro shiga cikin daki, hakan zai sa ba za su ciji mutane su yada cutar ba. Saboda sauro ba su jin magani sannu a hankali, shi ya sa magungunan kashe kwari da kuma sauran maganunan kasha sauro ba sa aiki yadda ya kamata. Watakila wannan sabon sakamakon nazari zai taimaka wajen yin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro.

Amma duk da haka, masu nazarin sun ce, ko kyautata ingancin gidaje zai iya taimakawa wajen yin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro, ko a’a, ya dogara da mabambantan wurare. Alal misali, galibi dai sauro su kan shiga dakuna su ciji mutane a cikin duhun dare, amma a wasu wurare, cutar zazzabin cizon sauro ta kan yadu a wajen daki. Saboda haka gidajen zamani ba su yi aiki wajen yin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro kamar yadda ake zato ba a wadannan wurare.

Adadin kididdigar da hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta kaddamar ya shaida cewa, yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara, yanki ne inda cutar zazzabin cizon sauron ta fi yaduwa a duniya. Yanzu haka yin amfani da gidan sauro da ke da magani a jikinsa, da kuma fesa sinadarin kashe kwari a daki, su ne matakai biyu da WHO ta ba da shawara a dauka don maganin sauro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here