Najeriya ta musanta gaza biyan bashin China sakamakon tasgaro ga sifurin jirgin kasa

0
109

Ofishin kula da basussuka na Najeriya, ya musanta zargin cewa gwamnatin tarayya ta gaza biyan kuɗin ruwa ga China don samun bashi.

Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito cewa an ci tarar Najeriya $90m bayan bashin da China ke bin ta ya ƙaru zuwa dala miliyan 240 a cikin shekaru biyu da suka gabata.

An ce an karɓo bashin ne domin gyara wasu layukan dogo a ƙasar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, DMO ya musanta rahotannin, inda ya ce Najeriya ta jajirce wajen ganin ta mutunta bashin da ake bin ta, kuma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen biyan basussukan da ta ciyo.

Sanarwar ta kara da cewa, “Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen ganin ta biya bashin da ake bin ta a kan lokaci.”

Don haka ofishin ya bukaci jama’a da su yi watsi da rahotannin.

Ya zuwa watan Disamba na 2021, DMO ya ce, bashin da China ke bin Najeriya ya kai dala biliyan 4.1, sai dai bai yi ƙarin haske ba kan yawan bashin da Najeriya ta ciyo ba daga ƙasar China ba zuwa yanzu.

A shekarun baya-bayan nan dai Najeriya ta yi asarar kuɗin shiga sakamakon yawaitar hare-haren da ake kai wa kan hanyoyin jiragen kasa da kuma sace fasinjojin da ya yi sanadiyar dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasa a wasu hanyoyin na ɗan wani lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here