Sama da mutum 80 sun mutu yayin turmutsutsun rabon kayan Sallah

1
347

Wani hoton bidiyo da aka watsa a kafafen sada zumunta ya nuna yadda mutane suka shiga ruɗani a wajen wata makaranta da aka samu mutuwar mutum 80 a turmutsusun rabon kayan sallah a Bab al-Yemen da ke Sanaa, babban birnin ƙasar.

Akwai kuma ƙarin mutane da suka jikkata – ciki har da mutum 13 waɗanda ke asibiti cikinn mawuyacin hali, a cewar jami’ai.

Ɗaruruwan mutane ne ciki har da ƙananan yara suka taru a wata makaranta domin karɓar tallafin kayan sallah.

Wani mai magana da yawun ma’aikatar cikin gida na kungiyar Houthi, ya ɗora laifin turmutsusun kan rashin tsari mai kyau na rabon tallafin daga wajen jami’ai.

Sai dai shaidun gani da ido biyu, sun bayyana cewa mayakan ƴan Houthiu sun yi harbi a iska a wani yunkuri na shawo kan dandazon mutane da suka taru, inda hakan ya jawo wayoyin wutar lantarki suka haɗu tare da fashewa da kuma kawo ruɗani a cikin mutane.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here