Bikin Sallah: Dauda Lawal ya taya Musulmai murna, ya nemi a dage da addu’a

0
271

Zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Dauda Lawal ya aike da saƙon taya murna ga ɗaukacin al’ummar Musulmi na Jihar Zamfara da ma faɗin Nijeriya bisa ganin ƙarshen watan azumin shekarar 1444 da kuma bikin sallah.

Lawal a wata takardar sanarwa da ofishin zaɓaɓɓen gwamnan ya fitar, wanda Sulaiman Bala Idris ya sa wa hannu, ya buƙaci al’ummar Jihar Zamfara su zage damtse wurin yin addu’o’i don wanzuwar zaman lafiya a faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa, watan Ramadana zaɓaɓɓen wata ne daga Allah (SWT) a matsayin watan yin azumi da kuma tsarkake zukata.

Sanarwar ta ci gaba da bayanin cewa, “Ina taya ɗaukacin al’ummar Jihar Zamfara murnar wannan muhimmiyar rana mai albarka ta Idi, wanda shi ne ya kawo mu ƙarshen wata mai alfarma na azumin Ramadana.

“Sallar Idi rana ce ta farin ciki da godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa irin ni’imar da ya yi mana na ganin kammaluwar wata mai alfarma.

“Rana ce da za a gode wa Allah (SWT) da ya bamu ikon yin ibadar azumi a matsayin ibada kamar yadda addini ya umurta a cikin Al-Ƙur’ani mai girma. Mun yi ibada tare da sake samun kusanci da Allah.

“Jiharmu tana cikin matsanancin hali na buƙatar addu’a da fata nigari. Dole ne mu ƙaunaci juna. Haka nan kuma dole ne mu ci gaba da rayuwa da darussan da muka koya daga watan Ramadan, musamman ma zaman lafiya.

“Kada kuma mu manta da ci gaba da yin addu’a a kodayaushe don ganin dawowar zaman lafiya a jiharmu mai albarka.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here