Najeriya na nazari don ganin harkokin rayuwa ba su durƙushe ba idan an cire tallafin mai

0
82

Gwamnatin Najeriya ta ce tana nazari a kan hanya mafi dacewa ta cire tallafin man fetur, ba tare da an kawo cikas ga harkokin rayuwa a ƙasar ba.

Babban sakatare a ma’aikatar albarkatun man fetur, Ambasada Gabriel Aduda ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi ga manema labarai a ƙarshen Taron Ƙoli kan Makamashi na Duniya a Najeriya.

Ya ce gwamnati tabbas ta duƙufa kan aniyar cire tallafin man fetur, amma ba ta sa ranar yin hakan ba, don kuwa sai ta gama nazarin duk alƙaluma da nufin ganin raɗaɗin da lamarin zai kawo, bai kasance mai tsanani ga masu ƙaramin ƙarfi a Najeriya ba.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Aduda na cewa ko da yake cire tallafin man fetur abu ne da aka mayar da hankali kansa tsawon lokaci, amma Shugaba Buhari kuma ministan albarkatun mai yana ɗaukar lamarin da gaske, kuma yana tuntuɓar kowa da kowa a ɓangaren samar da mai.

A cewarsa har yanzu, jami’an gwamnati na duban tsanaki kan yadda za a cire tallafin ba tare da al’amuran raryuwa sun hargitse ba.

Ya ce nauyi ne a kansu a matsayinsu na gwamnati, don haka tabbas sai sun kawo matakan da za su rage raɗaɗi kuma a samar da canjin ƙasashen waje ta yadda ‘yan kasuwa za su iya samu cikin sauƙi don shigo da kayan da ake buƙata.

Gabriel Aduda ya tabbatar da cewa sai sun samar da kuɗaɗen canjin waje na aƙalla wata shida ta yadda ko an samu akasi, rayuwa ba ta tagayyara ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here