Rundunar RSF ta amince ta tsagaita wuta ta awa 72

0
107

Rundunar sa-kai ta Sudan, Rapid Support Forces [ko RSF] ta amince ta tsagaita wuta ta awa 72 domin bari a gudanar da ayyukan jinkai daga karfe shida na safiyar Juma’a a agogon Khartoum.

“Wannan tsagaita wuta ta zo daidai da lokacin da ake bikin karamar Sallah… domin bayar da dama ga masu aikin jinkai su kwashe mutane da kuma ba su damar zuwa domin gaishe da iyalansu,” in ji wata sanarwar da RSF ta fitar ranar Juma’a.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa an yi ta harba bama-bamai da yin luguden wuta awanni kafin fitar da wannan sanarwar.

Wani jami’in Hukumar Lafiya ta Duniya Ahmed al Mandhari ya ce mutum “kusan 330 sun mutu” sakamakon rikicin.

Kawo yanzu shugaban rundunar sojin kasar Janar Abdel Fattah al Burhan, bai ce uffan game da sanarwar ba a wani sako da ya wallafa a shafin Facebook na rundunar sojin.

Ranar Alhamis, Janar al Burhan ya ki amincewa ya tattauna da RSF sai dai ya ce kofarsa a bude take ya yi sulhu.

Shugabannin wasu kasashe irin su Shugaba Erdogan na Turkiya, da ministocin kasashen waje na Saudiyya da Qatar da babban jami’in hukumar leken asiri ta Masar da takwaransa na Amurka sun kira Janar Burhan ta wayar tarho inda suka bukaci a tsagaita wuta.

A yayin da ake cigaba da fafatawa, Burhan ya yi watsi da bukatar tattaunawa da shugaban RSF Mohamed Hamdan Daglo, inda ya shaida wa gidan talbijin na Al Jazeera cewa babu zabin da ya rage masa wanda ya fi yin amfani da “karfin soji” don murkushe RSF.

‘Muna roko a ba mu damar kwashe ‘ya’yanmu’

Gwamnatin Nijeriya ta bi sahun sauran kasashen duniya wurin kira ga bangarorin da ke rikici da juna a Sudan su tsagaita wuta.

Wata sanarwa da ma’aikatar wajen kasar ta fitar ranar Alhamis ta gwamnati “ta yi matukar kaduwa game da ta’azzarar rikicin Sudan” wanda ya jefa farar-hula cikin mawuyacin hali.

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta bukaci takwararta ta Sudan ta ba ta damar kwashe dalibai da sauran ‘ya’yanta da ke kasar.

Ta ce ma’aikatar wajen kasar ta samar da dandali a manhajojin WhatsApp da Telegram yadda ‘ya’yanta za su sanar da halin da suke ciki domin a dauki mataki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here