An sanar da ranakun kwantan wasan Man United a Premier

0
89

Mahukuntan Premier League sun sanar da ranakun da Manchester United za ta buga kwantan wasanta biyu a gasar.

Hakan ya biyo bayan da aka fitar da United daga gasar zakarun Turai ta Europa League ta 2022/23.

Ranar Alhamis Sevilla ta doke United 3-0 a Sifaniya a wasan farko a daf da karshe a Europa, tun farko sun tashi 2-2 a Old Trafford.

Kungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama za ta karbi bakuncin Wolverhampton a Old Trafford ranar 13 ga watan Mayu.

Mako daya tsakani wato ranar 20 ga watan Mayu, United za ta ziyarci filin Vitality, domin kece raini da Bournemouth.

A wasan farko a Premier League, United ta ci Wolverhampton 1-0 ranar 1 ga Kirsimeti, kuma Marcus Rashford ne ya ci kwallon a zagaye na biyu.

Haka kuma a karawar farko da United ta yi a 2023 ta doke Bournemouth 3-0 a Old Trafford, wadanda suka ci kwallon sun hada da Luke Shaw da Casemiro da kuma Rashford.

To sai dai ba a tsayar da ranar da ya kamata United ta karbi bakuncin Chelsea ba a gasar Premier da ya kamata su buga ranar Lahadi 23 ga watan Afirilu.

United za ta buga wasan daf da karshe a FA Cup da Brighton ranar Lahadi a Wembley, dalilin da aka dake fafatawar da ya kamata ta yi da Chelsea.

United wadda take ta ukun teburi da maki 59 za ta ziyarci Tottenham ranar 27 ga watan Afirilu, karawar karshe a bana da United za ta iya ita ce Fulham ranar 28 ga watan Mayu.

Wasannin Premier League da suka rage wa United:

  • Alhamis 27 ga Afirilu: Tottenham wasan waje
  • Lahadi 30 ga Afirilu: Aston Villa wasan gida
  • Alhamis 4 ga Mayu: Brighton wasan waje
  • Lahadi 7 ga Mayu: West Ham wasan waje
  • Asabar 13 ga Mayu: Wolves wasan gida
  • Asabar 20 ga Mayu: Bournemouth wasan waje
  • Sun 28 da Mayu: Fulham wasan gida

Za a sanar da ranar da United za ta kece raini da Chelsea a Premier a Old Trafford nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here