Da kuɗin haram aka gina mafi yawan rukunin gidajen Abuja – EFCC

0
77

Hukumar da ke Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Najeriya ta’annati EFCC ta ce a yanzu za ta mayar da hankali kan waɗanda ke fakewa da gina rukunin gidaje wajen halasta kuɗin haram da sauran laifukan da suka shafi kuɗi.

Yayin da yake jawabi a wajen taron haras da ‘yan jarida kan yadda za su riƙa bayar da ingantattun rahotonni kan laifukan da suka shafi kuɗi da tattalin arziki a birnin Benin na jihar Edo, lauyan hukumar Chris Mishela ya ce da yawa daga cikin rukunin gidajen da ake ginawa a Abuja da Legas da sauran yankunan ƙasar, ana gina su ne da kuɗaɗen haram.

Ya ƙara da cewa, ”akwai rukunin gidaje masu yawa a Abuja, waɗanda muka yi amanna cewa an samu kuɗin gina su ta haramtattun hanyoyi”.

”Kuɗaɗen haram da yawa da aka samu ta ɓangaren gwamnati ko wasu miyagun laifukan da suka shafi kuɗi na duniya, ana amfani da su wajen kasuwancin rukunin gidaje”, in shi.

”EFCC na aiki domin bincike da kuma lura da wannan ɓangare, kuma sabuwar dokar halasta kuɗin haram ta bai wa gwamnati damar lura da bincike kan rukunin gidaje, kuma EFCC na ƙarƙashin gwamnati don haka muna aiki da dokar”.

“Ba iya binciken kawai muke yi ba, mun ma gano cewa wasu daga cikinsu an gina su ne da kuɗin haram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here