Dalilan da suka sa Messi ya shiga jerin mutum 100 masu daraja a duniya

0
109

Dan Wasa Messi kuma kyaftin din tawagar Argentina, Lionel Messi ya shiga cikin jerin ‘yan wasa 100 mafi tasiri a shekarar 2023 a fannin wasanni da kamfanin jaridar TIMES ta lissafa.

Cikin shekarar 2022, dan wasan Paris St German ya ja ragamar Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya, kuma na uku jimilla da kasar ta dauka, matakin da ake ganin babba duba da sukar da ya sha a baya na rashin tabuka abin arziki a kasar ta Argentina.

Daman kofin duniya ne kadai Messi bai dauka ba daga cikin manyan gasar duniya a tarihinsa na buga wasa bayan lashe kofuna da dama da suka hada har da kofin zakarun turai.

Argentina ta dauki kofin a cikin Disamba a Katar a bugun fenariti da ci 4-2 a kan Faransa mai rike da na 2018, bayan da suka tashi 3-3 kuma dan wasan ya taka muhimmiyar rawa.

‘Yar wasan zamiyar kankara ‘yar Amurka, Mikaela Shiffrin tana cikin jerin ‘yan wasa 100 a 2023 da suka fi tasiri a fannin wasanni bayan da a kakar nan Shiffrin ta kafa tarihin lashe gasar zamiyar kankara da duniya da cin wasa 88, ta zarta nasara 86 da Ingemar Stenmark ke da shi a tarihin a baya.

Tsohon zakakurin dan wasan kwallon tennis, Roger Federer ya ce Messi dan wasa ne na daban, wanda ke sawa a kalli wasa ko ba ka sha’awar wasan kuma ya kafa tarihi babba a duniya.

Wasu daga cikin ‘yan wasa 100 mafiya tasiri a 2023 da TIMES ta bayyana sun hada da wanda ya dauki kofi biyu a Super Bowl, Patrick Mahomes. sannan akwai ‘yar Amurka mai wasan kwallon kwando, Brittney Griner da dan kwallon tawagar Faransa, Kylian Mbappe da mai rike da Grand Slam uku a tennis Iga Swiatek.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here