Hukumomin lafiya a Argentina sun sanar cewa an ƙara samun mutanen da suka mutu sanadin zazzaɓin denge a ‘yan kwanakin nan.
Argentina ce ta taɓa samun ɓarkewar zazzaɓin denge mafi muni da yawan mutanen da suka kamu a Kudancin Amurka
Sai dai mace-macen da aka samu sanadin zazzaɓin da ya sake ɓulla a bana sun disashe na baya.
Tun a farkon wannan shekara, a cewar jami’an lafiya, mutum 45 suka mutu yayin da wasu fiye da 65,000 suka kamu da zazzaɓin.
Denge, wani zazzabi ne mai saurin yaɗuwa kuma sauro ne yake haddasa shi.
Hatsarin zazzaɓin shi ne a mafi yawan lokuta, ba a ganin alamomin cuta, sai dai ƙwayar cutar sau da yawa tana iya kai wa ga mutuwa.