Gwamnatin Ganduje ta cancanci yabo — Sarkin Kano

0
144

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje nai barin gado ya yi abin a yaba a tsawon shekara takwas da ta yi yana mulkin jihar.

Sarkin Kano ya ce Jihar Kano ta samu gagarumin cigaba a zamanin mulkin Ganduje, kuma Masarautar Kano ta ba wa gwamnan cikakken goyon baya domin samun haka.

A cewar sarkin, Ganduje ya kirkiro tare da aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba da dama wadanda suka shafi rayuwar Kanawa ta kyawawan fuskoki.

Ya bayyana haka ne a jawabinsa na Hawan Nasarawa, inda ya ziyarci gidan gwamnaitn jihar a ranar Lahadi.

Sakataren yada labaran gwamnan, Hassan Musa, ya ruwaito cewa Sarkin Kano ya bayyana godiya ga gwamnan bisa yadda ya ba shi damar zama maganin kakanninsa, a kan sarautar Kano.

“Ba za mu taba manta irin alherin da ka yi mana ba. Muna rokon Allah Ya ci gaba da daukaka ka, Ya yi maka jagora a cikin duk al’amuranka,” in ji sarkin.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito, ya ruwaito sarkin yana kira ga al’ummar masarautar da su bayar da hadin kai ga aikin kidayan jama’a da za a gudanar a watan Mayu.

A nasa bangaren, Gwamnan Ganduje, wanda mataimakinsa, Nasiru  Yusuf Gawuna, ya wakilta, ya yaba da irin goyon bayan da Masarautar Kano ta ba shi domin gudanar da ayyuka da shirye-shiryen gwamnati cikin nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here