An yi waje da kungiyar su Ronaldo, Al-Nassr a gasar cin kofin Saudiya

0
167

Bayan da suka doke abokan karawarsu da ci 4-0 watanni biyu da suka gabata a gasar lig na Saudiya- wasan da Ronaldo ya ci dukkan kwallaye hudu – ana sa ran masu masaukin baki za su kai ga wasan karshe don karawa mai zafi da Al-Hilal, sai gas hi an yi waje da su.

Dama kwallo daya kachal Wehda ke nema don hayewa zuwa wasan karshe, wajen fitar da Nassr na Ronaldo daga gasar a matakin wasan kusa da na karshe.

Ronaldo ya yi ta kai farmaki tare da baras da damarmaki da dama na cin kwallo, a fafatawar da suka karkare da ‘yan wasa goma saboda jan kati da Abdullah Al-Hafith ya samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here