Home Labarai Wasanni Tottenham ta kori kocinta Stellini bayan doke su da Newcastle ta yi...

Tottenham ta kori kocinta Stellini bayan doke su da Newcastle ta yi da ci 6 – 1

0
122

Stellini, wanda aka nada shi ne a watan jiya bayan tsohon mai gidansa Antonio Conte ya bar kungiyar, kuma tuni Ryan Mason ya maye gurbinsa nan ta ke.

Mataimakin Conte na dogon lokaci nasara daya kachal daga cikin wasanni hudu da ya jagoranta, ya haifar da cikas ga damar Spurs zuwa gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.

Har yanzu Tottenham na matsayi na biyar a teburin Premier amma maki shida ne tsakaninta da ta hudu kuma da sauran akalla wasa daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

X whatsapp