’Yan matan Chibok’ 2 sun gudo daga hannun Boko Haram

0
122

Karin mutum biyu daga cikin daliban Makarantar Sakandaren ’Yan Mata da ke Chibok a Jihar Borno sun gudo daga hannun mayakan Boko Haram da suka sace su shekaru tara da suka gabata.

Majiyoyin tsaro da mazauna Jihar Borno sun shaida wa wakilinmu cewa matan su biyu sun samu tserewa a dalilin tsananta luguden wuta da sojoji suke yi a kan sansanonin kungiyar da ke Dajin Sambisa.

Wata majiyar tsaro ta ce daliban da suka gudo su ne Hauwa Mutah da kuma Esther Markus.

Ta bayyana cewa, “Daya daga cikinsu ’yar kauyen Chibok ce, dayar kuma ’yar kauyen Dzilang ce.”

Kawo yanzu daliban makarantar 96 ne suka rage a hannun kungiyar Boko Haram da ta sace su tun a watan Afrilun shekarar 2014.

Mako biyu da suka gabata, rundubar soji ta Operation Hadinkai da ke yaki da kungiyar, ta bayyana cewa akwai saura mutum 98 daga cikin Daliban Chibok a hannun kungiyar.

Kwamandan Sashen Lelen Asiri na rundunar, Kanar Obinna Ezuipke ya ce, “Daga cikin Daliban Chibok 276 da aka sace, 57 sun tsere a 2014, an sako 107 a 2018.

“An ceto wasu uku 2019 da biyu a 2021 sai wasu tara a 2022, wanda jimilla 178 ke nan, saura 98 da suka rage a hannun Boko Haram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here