An harbe babban malamin Musulunci a Iran kuma wakili a Majalisar Ƙwararru mai karfin iko

0
96

An harbe wani babban malamin addinin Musulunci a Iran kuma wakili a Majalisar Ƙwararru mai ƙarfin iko a wata jihar arewacin ƙasar.

Wata kafar yaɗa labaran ƙasar ta ce Ayatollah Abbasali Soleimani ya mutu a asibiti bayan harbin da aka yi masa a banki da ke Babolsar, cikin lardin in Mazandaran.

Kamfanin dillancin labaran Iran IRNA ya ce an kama mutumin da ya kai harin amma ba a iya fayyace manufarsa ba..

Ayatollah Soleimani yana ɗaya daga cikin malaman shi’a 88 a Majalisar Ƙwararru, wadda ke naɗa Jagoran Addinin Iran kuma – a ƙa’ida – suna iya tuɓe shi.

A baya, ya taɓa zama mataimaki na musamman ga Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei a lardin Sistan-Baluchistan na kudu maso gabashin ƙasar mai fama da rikici, kafin ya sauka daga muƙamin a 2019 bayan ya shafe tsawon shekara 17.

An ba da rahoton cewa Ayatollah Soleimani, wanda ya haura shekara 70, yana zaune ne a wani reshe na Bankin Melli da ke garin Babolsar da safiyar Laraba lokacin da aka harbe shi.

Kafar labarai ta Hawzahnews, ta ambato wani shaida yana cewa wani mutum ne ya warci bindigar wani jami’in tsaron bankin kuma ya buɗe wuta.

A watan Afrilu ma, an kashe malamai guda biyu kuma aka raunata na uku a wani harin wuƙa da aka kai wani wurin ibadar ‘yan shi’a a arewa maso gabashin birnin Mashhad.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here